Gwamantin taraiyya ta ce ta kashe zunzurutun kudi har naira milyan 560 domin jigilar ‘Yan Najeriyan da suka makale a kasar Sudan ta cikin motocin safa, zuwa wuraren da suke da amince da za’a iya dauko su ta cikin jirgin zuwa gida Najeriya, biyo bayan yakin da ya barke a kasar ta Sudan.
Ministan harkokin kasashen Waje Geofrrey Onyeama ne ya baiyana haka a ranar Laraba , Lokacin da yake amasa tambayoyin manema Labarai na fadar shugaban kasa a Abuja, Ya kuma kara da cewar babu wani Dan Najeriya da ya rasa ransa saboda yakin da ake yi a kasar.
Ya kara da cewar za’a dauki tsawon kwanaki biyu kafin kammala kwashe ‘Yan Najeriyar da suka makale a kasar ta Sudan, Bugu da kari ya ce da zarar an kammala kaisu kasar Masar, za’a yi tsare-tsaren da suka dace domin dauko su ta cikin jirgi zuwa gida Najeriya.
Ya kuma cewar za’a bayar da kulawa ta musamman ga Mata da kananan yara kafin a kaiga saka jami’an Diflomasiyyar kasar nan wadanda suma suna cikin mutanen da za’a kwaso.