Wani binciken sirri ya gano cewa kungiyar mayakan ISWAP dana Boko Haram na shirin kai hare-hare a wasu jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Yammacin kasar nan.
Rahotanni na baiyana cewa hukumomin tsaro sun samu rahotonnin sirri na karkashin kasa dake baiyana cewa mayakan na ISWAP da Boko Haram sun shirya kai hari jihohin Legas, Kaduna, Kogi, Katsina da Zamfara da kuma Abuja babban birnin tarayya.
Wata sanarwa da ta fita daga shalkwatar Rundunar tsaro ta CIVIL DEFENCE, a ranar Talata, ta sanar da jihohin da abun ya shafa kan yiyuwar kai masu hare-haren, To Sai dai kuma kakakin hukumar Shola Odumosu, ya musanta cewa wasikar daga wajensu ta fitar.
Sai dai wani kwamandan rundunar dake waa jiha a kasar nan, wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya tabbatar wa jaridar Punch takardar da rundunar ta fitar, ya ce an umurci jami’an tsaro da su yi gum da bakinsu domin kada al’amarin ya haifar da rudani a tsakanin jama’a.