Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ayyana yau Laraba 4 ga watan Oktoba 2023 a matsayin ranar hutu domin zagayowar ranar takutaha da ake murnar tunawa da ranar sunan haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Alhaji Baba Halilu Dantiye ya fitar a safiyar yau Laraba.
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokacin domin yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da sanya su cikin harkokinsu na yau da kullum.
Ya kuma bukaci jama’a da su rika yin addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba a Kano da Najeriya baki daya.
Ya yi addu’ar Allah ya shiga al'amuranmu a wannan lokaci mawuyaci, ya kuma bamu albarkacin wannan damuna da kuma lokacin mai zuwa.