Tsohon shugaban cibiyar bincike kan harkokin aikin gona ta jami’ar Ahmadu Bello Zaria, farfesa Ibrahim Umar Abubakar, ya baiyana rashin tsaro amatsayin babban dalilin da suke haddasa rashin abinci a kasa.
Masanin ya baiyana haka ne a yayin da yake gabatar da wata mukala,a yayin wani taro kan aikin gona da kwalejin Fasahar aikin gona ta gwamnatin taraiyya dake Hotoro a jihar Kano ta shirya.
Farfesa Abubakar ya kara da cewa aiyukan ‘yan ta’adda sun gurgunta aiyukan gona kamar noma da kamun kifi da kuma sauran dabbobi, wanda hakan yasa abune mai wahalar gaske yin jigilar kayan da aka noma daga wani bangare zuwa wani sashi na kasar nan.
Da yake zantawa da wakilinmu bashir Faruk Durumin iya, Shugaban kwalejin, Dr Muhammad Yusha’u Gwaram, ya baiyana cewa kwararru zasu gabatar da mukaloli kimanin 70 a yayin taron, wadda za’a wallafa a farkon shekara mai zuwa, domin bayar da gudunmuwa a matayin abun koyo ga Dalibai da kuma sauran kwararru.