Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi hasashen cewa hauhawar farashin kayayyaki zai rage habakar tattalin arzikin Najeriya zuwa kashi 2.9 cikin 100 a shekarar 2023.
Matsalar zata rage hasashen ci gaban tattalin arzikin kasarnan da kashi sifili da digo 3 zuwa kashi 2.9 cikin 100 a shekarar 2023 sakamakon rauni da aka samu wajen samar da mai da iskar gas.
IMF ya bayyana hakan a cikin sabon hasashen tattalin arzikin duniya na watan Oktoba wanda aka sabunta ranar Talata.
A farkon watan Yuli, Asusun IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa da kashi 3.2 cikin 100 a shekarar 2023.
Sai dai a sabon hasashen da ya yi, ya ce tattalin arzikin na Najeriya ya cigaban zai raguwa daga kashi 3.3 a shekarar 2022 zuwa kashi 2.9 a shekarar 2023.