On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Matsalar Satar 'Danyen Mai Zata Kawo Cikas Wajen Aiwatar Sabuwar Dokar Masana’antar Man Fetur A Najeriya - Majalissar Dattijai

Majalisar Dattawan kasarnan, ta ce yawaitar satar mai da ake fama da ita a Najeriya, ka iya kawo cikas wajen aiwatar da dokar masana’antar Man Fetur da Majalisar ta amince da ita a bara idan ba a gaggauta magance matsalar ba.

Shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar dattijai da ya binciki batun satar man fetur da tasirin hakar man fetur da kuma kudaden shigar mai, Sanata Akpan Bassey, ya bayyana haka a jiya, a wani zaman bincike na kwana daya kan al’amarin.

Basseys ya koka kan yadda ake yawan satar danyen mai a yankunan da ake hako mai a yankin Neja-Delta tare da bayyana cewa hakan na gurgunta tattalin arzikin kasa.

Shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan, wanda ya bayyana bude taron jin ra’ayin jama’a akan al’amarin, ya ce majalisar za ta kasance bata da wani zabi da ya rage Illa ta fara bayyana masu aikata laifin kafin watan Disamba na shekarar da muke ciki.