Matashin dan siyasa mai rajin inganta ilimi a Jihar Kano, Injiniya Yusuf Abdullahi Da'awa, ya kaddamar da taron sanya yara marasa galihu guda 1300 a makaranta, tare da samar musu da kayan makaranta da sauran ababan koyon karatu.
Matashin wanda ke takarar dan majalisar wakilai mai wakiltar birni da kewaye, karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya ce manufar bada tallafin ita ce samar da Karin damar zuwa makaranta ga yaran da iyayen ba su da karfin daukar nauyin karatun su.
A cewar sa, "babu yadda za a magance tarin matsalolin dake damun al'umar mu, ba tare da an samar da wata dama da yara zasu samu ilimi ba, ba tare da la'akari da nauyin aljihun iyayen su ba."
"Allah ya sani ni dan talakawa ne kuma ina alfahari da damar da Allah ya bani ta taimakawa al'uma, kuma babban buri na shine, yadda muka hadu a nan a ce bayan wasu shekaru an samu wasu daga cikin wadannan yara sun tara wasu yayan talakawa domin daukar nauyin karatun su, ko da rai na ko babu."
Daga nan Injiniya Yusuf Abdullahi, wanda ya kasance mafi kankantar shekaru cikin jerin 'yan takarkaru masu neman sahalewar al'umar su domin su wakilce su a majalisar wakilai ta tarayyar kasar nan ya kara da cewa, tun kafin ya fara neman takara ya fara kokarin taimakawa yayan marasa karfi domin su samu ilimi kamar kowa.
Ya ce, "a baya mun dauki nauyin karatun dalibai da dama wajen rubuta jarabawar WAEC da NECO da kuma JAMB tsahon shekaru da suka wuce."
"Hakan kuwa na da nasaba da nazari da muka yi akan alkaluma da ke nuni da cewa wani kaso mafi tsoka na dalibai kan hakura da cigaba da karatu saboda gazawa wajen samun kudin wadannan jarabawoyi, shiyasa muka dukufa wajen ganin cewa mun yi iya yin mu wajen tabbatar da cewa mun tallafi karatun dalibai da dama a fadin wannan karamar hukuma."
Ya kuma kara da cewa nan gaba kadan zai sake kaddamar da shirin koyar da sana'o'in dogaro da kai ga mata da matasa, domin rage radadin tattalin arziki da ake fama da shi.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron, akwai tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa, Ghali Umar Na'abba da jigo a jam'iyyar PDP a nan Kano, Ibrahim Aminu Dan'iya da ma sauran manyan masu ruwa da tsaki na karamar hukumar birni da dama.