Matasan da suka kammala makarantar koyar da dabarun tsaro dake garin Zakirai a karamar hukumar Gabasawa, na rokon daukin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samar musu da guraben ayyukan yi domin tallafa wa harkar tsaro da zaman lafiya a Jihar ta Arewa maso Yammacin Najeriya.
Shugaban kungiyar daliban, Kamalu Auwalu Ibrahim, wanda ya yi wannan roko a madadin daliban da suka kammala karatu a makarantar, ya ce a makarantar an koyar da su dabarun tsaro tare da alkawarin za a ba su ayyukan yi bayan sun kammala horon.
Auwalu ya kara da cewa sama da matasa 200 sun samu horo da dabarun tsaro, wanda zai taimakawa kokarin hukumomi a fannin tsaro da masu ruwa da tsaki wajen dorewar zaman lafiya.