On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mataimakin shugaban Najeriya Ya Tafi Kasar Canada Domin Ziyarar Aiki Ta Kwana Uku Mai Cike Da Tarihi

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bar Najeriya domin ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Canada.

Mai magana da yawunsa, Laolu Akande, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, yace wannan ita ce ziyarar manyan jami’an gwamnati  ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai kasar Kanada tun shekara ta 2000 lokacin da shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ziyarci kasar.

Ana saran mataimakin shugaban kasar zai gana da Chrystia Freeland, mataimakiyar firaministan kasar Canada, da wasu manyan 'yan majalisar dokoki a birnin Ottawa a yau.

Daga bisani  zai gabatar da mukala  ga jama'a a Jami'ar Queen  ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, mataimakin shugaban na Najerya zai kuma gana da shugabannin ‘yan  Najeriya da wakilan 'yan kasuwa da masu zuba jari na Kanada.

Ana sa ran zai dawo Abuja nan da mako mai zuwa.