Shugaban Hukumar zabe ta kasar Kenya ya aiyana mataimakin shugaban kasar William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar , bayan doke abokin karawarsa Raila Odinga wanda yay i takarar shugabancin kasar har sau biyar.
Sai dai kuma tun gabanin aiyana sakamakon zaben na karshe ne,mataimakin shugaban hukumar zaben kasar Kenya, da kuma wasu kwamishinoni hukumar ukku suka fadawa Manema Labarai cewa ba zasu goyi bayan sakamakon zabe da aka yi rufa-rufa a cikinsa ba.
Rabuwar kan da aka samu a hukumar zaben ta zo ne ‘yan mintoci, bayan da wakilin Raila Odinga yace ba zasu iya faiyace sakamakon zaben ba, sannan kuma sunyi zargin an tafka lefukan zabe, amma bai yi wani karin haske ba.
Raila Odinga.
Abunda ya rage ga al’ummar kasar Kenya a halin yanzu , shine dakon ko Mister Raila Odinga zai garzaya gaban kotu domin kalubalantar sakamakon zaben na ranar Talar makon jiya da aka yi cikin kwanciyar hankali da lumana.