Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bukaci shugabannin duniya dasu jingine banbancin dake tsakaninsu tare da yin aiki tare, domin murkushe aiyukan ta’adanci a nahiyar Afrika.
Osinbajo ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a yayin wata mukala da aka gabatar a kwalejin Kings dake birnin London,inda ya koka kan yadda aiyukan ta’addanci suka yi kamari a yankin Sahel na Afrika.
Ya baiyana cewar aiyukan ta’adanci sun haifar da tarin matsaloli,inda y ace kamata yayi shugabannin duniya su fahimci cewar matsalar aiyukan ta’adanci a wani bangare na duniya, matsala ce data shafi dukkanin ‘yan adam.
Bugu da kari mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi kira da a kawo karshen rikicin dake faruwa tsakanin kasashen Rasha da Ukrain,tare da yin kira ga kasashen Afrika dasu tashi haikan wajen ganin sun dogara da kansu ta bangaren samar da abinci.