Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima tashi daga Abuja zuwa kasashen Italiya da Rasha, domin wakiltar shugaban kasa, Bola Tinubu a wasu manyan taruka biyu na duniya da za’a gudanar.
A kasar Italiya mataimakin shugaban kasar zai bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya domin yin taro akan kirkiro hanyoyin bunkasa samar da abinci a duniya, wanda za’a fara gabatarwa daga yau zuwa ranar Laraba, Daga nan ne kuma mataimakin shugaban kasar zai zarce zuwa kasar Rasha, domin wakiltar shugaban kasar, kan taron da za’a yi tsakanin Rasha da kasashen Afrika daga ranar laraba 26 ga watan da muke ciki zuwa Asabar 29 ga watan da muke ciki.
Zai tattauna da ‘yan siyasa da manyan ‘yan kasuwa a taron da za’a yi wanda zai mayar da hankali kan kyautata alaka tsakanin Rasha da sauran kasashen Afrika, da kuma sauran batutuwa.