On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Tafi Kasar Afrika Ta Kudu

KASHIM

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima zai yi balaguro zuwa birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu, domin wakiltar shugaban kasa, Bola Tinubu a taron Shugabannin kungiyar kasashen BRICS karo na 15.

Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin  shugaban kasa, Olusola Abiola ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin a Abuja.

Mataimakin shugaban kasar zai  bi sahun sauran  shugabannin kasashe da ‘yan kasuwa da kuma  ‘yan siyasa  daga sassa daban daban na duniya a yayin taron da za’a yi a cibiyar taro  ta Sandton dake birnin  Johannesburg  daga yau 22 ga wata  zuwa  24 ga watan da muke ciki.

Taron kasashen kungiyar BRICS, ya kunshi kasashen Brazil da Rasha da India sai China da  Afrika ta kudu  wanda suka cure  wuri  daya  a kokarin da  inganta tattalin arzikin duniya.