Mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman,Ya yi murabus daga kan kujerarsa, biyo bayan yunkurin shugaban kasa, Bola Tinubu na dora tsohon gwmanan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje akan shugabancin jam’’iyyar na kasa.
Idan ba’a manta ba, Salihu Lukman ya fito ‘karara ya nuna adawarsa da sanar da Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, Inda ya ce daukar irin wanann mataki abune da ya ci karo da tsarin yadda iyayen jam’iyyar suka kafa ta.
Ya kuma baiyana cewar saukarsa daga kan kujerar ta fara aiki ne nan take, kuma ya dauki matakin ne sakamakon yanayin da jam’iyyar ta APC ta tsinci kanta a ciki.
Sai dai kuma ya sake jan kunnen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya guji yin amfani da abunda ya sabawa tsarin jam’iyyar wajen tafiyar da harkokinta.