Babu shakka abunda mutum ke tsammanin ana siyarwa a gidajen Mai shine man fetir , To sai dai a halin yanzu ta sauya zani, a yayin da wasu gidajen man a jihar Naija suka zama wuri hada-hada ta canjin kudi.
Hakan ya biyo bayan yadda a yanzu masu sana’ar POS abirnin Minnan jihar Naija suke siyan sabbin takardun kudi daga wajen masu gidajen man domin yin harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.
Wani mai sana’ar POS, mai suna Mohammed Isah ya fadawa manema Labarai cewa ya samu naira dubu 150 a ranar Asabar din data gabata, sannan kuma sake samun wata karin naira dubu 150 din a jiya, daga gidajen mai daban daban, domin ganin ya biyana bukatar abokan huldarsa.
Ya ce abunda mutum yake bukata shine kulla alaka da masu gidajen man domin samun kudin.