Kungiyar Masu sana’ar yin burodi ta kasa sun bayyana shirinsu tsayar da aiyukansu cak daga yau, domin nuna rashin jin dadinta kan yadda ake samun tashin farashin kayan da suke amfani dasu.
A cewar wata sanarwa da shugaban kungiyar, Emmanuel Onuorah ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, a halin yanzu an shiga yanayi na tasku wajen tafiyar da Gidan Burodi a kasar nan, sakamakon karuwar farashin kayayyakin da ake amfani dasu wajen samar da Burodin da kuma Man dizal da wuraren ke amfani dashi
Onuorah ya ce gidajen burodin suna yin gagarumar asara wanda hakan ba mai yuwa ba ne.
A cewarsa, burodi abinci ne na yau da kullum, kuma yana daya daga cikin abinci mafi arha a kasar nan, wanda Talakawa da Masu kudi ke amfani dashi.