Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban karamar hukumar Takum dake jihar Taraba, mai suna Boyi Manja, inda suka halaka dogarinsa a yayin harin da suka kai.
An sace shugaban karamar hukumar ne a garin Kofai Ahmadu dake kusa da kan hanyar Takum zuwa Wukari a ranar Lahadi.
Wani abokinsa wanda ya nemi a sakaye sunansa, Ya ce an harbe dogarin shugaban karamar hukumar ne a lokacin da suke musayar wuta tsakaninsa da masu garkuwar,Kafin su dauke shi.
Majiyar ta baiyana cewar shugaban karamar hukumar tare da mai tsaron lafiyar tasa da kuma Direbansa sun bar birnin Jalingo zuwa Takum ne, Inda masu garkuwar suka rika bin sawunsu.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar , Abdullahi Usman ya tabbatar da faruwar lamarin.