On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Masu Dillancin Shanu Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 9 Sanadiyar Arangama Da ‘Yan Kungiyar OPC A Jihar Kwara.

Shugaban kungiyar Fulani ta Gan Allah a Jihar Kwara, Ali Mohammed Jounwiro, ya ce an kashe mutane tara yayin da shanu 450 suka bata sanadiyyar rikicin da ya faru kungiyar OPC ranar Juma’a.

 

‘Yan kungiyar ta OPC da dillalan shanu sun yi arangama a kasuwar AjaseIpo da ke karamar hukumar Irepodun ta  jihar Kwara.

Da yake zantawa da manema labarai a daren jiya, Jounwiro ya yi zargin cewa ‘yan OPC sun sace sama da Naira miliyan 6 sanadiyar rikicin.

Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

Da yake mayar da martani, Jami’in kungiyar  OPC na jihar Kwara, Comrade Ganiyu Oladipupo, ya ce babu hannun mambobinsa a cikin rikicin.

Ya bayyana zargin da Jounwiro ya yi a matsayin wanda ba shi da tushe balle makama cewa OPC ta kashe dillalan shanu tara.