Ana saran masu ajiya a bankuna za su fara samun riba mai yawa a kan ajiyar su biyo bayan umarnin da babban bankin kasa CBN ya bayar ga dukkan bankunan da ake ajiya na su kara kudin ruwa daga kashi 10 zuwa 30 cikin dari.
A kwanakin baya ne CBN ya umurci bankunan da su rika biyan duk wani asusun ajiyar kudi ribar akalla kasha 4 da digo maimakon kashi 1.4 da ake biya a baya.
A wata takardar da daraktan sa ido kan harkokin bankuna na CBN Haruna B. Mustafa ya sanya wa hannu, babban bankin ya bayyana cewa an samu karin kudin ruwa a kan kudaden ajiya, bayan la’akari da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu.