Wasu daruruwan Maniyata aikin hajji sun gudanar da zanga-zanga a jihar Kano saboda rashin samun gurbin tafiya sauke farali a bana duk da cewa sun kammala biyan kudadensu karkashin shirin adashin gata ta bankin Jaiz.
Masu zanga-zangar su 284 sunyi tsinke a bankin Ja’iz dake Kano da kuma hukumar Jin dadin alhazai, sunce sun kadu matuka lokacin da suka fahimci cewa ba su da gurbi a cikin wadanda zasu tafiya kasa mai tsarki domin yin aikin hajjin bana duk da cewa duk kammala biyan kudinsu ta hanyar adashin gata da suka fara tun shekarar 2019.
Sai dai da yake martani akan al’amarin shugaban hukumar Jin dadin alhazai ta jihar Kano Muhammad Abba Dambatta, yace hukumar tana bakin kokarinta wajen ganin ta magance matsalar.
Ya kara da cewa babu gurbin sauke farali a bana ga wadanda suka biya kudi ta hanyara adashin gata musamman wadan suka biya ta bankin Ja’iz.