Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare, Ta baiyana cewar jirgin rundunar sojan sama ta kasa ya shirya tsaf domin dauko ‘yan Najeriyar da suka makale zuwa gida Najeriya, To sai dai har zuwa wannan lokacin iyakokin kasar Masar suna a kulle.
Bugu ta baiyana cewar tawagar jami’an rundunar sojin sama ta kasa sun tashi zuwa filin jirgin saman Aswan tun ranar Asabar din data gabata, domin kwaso mutanen, tare da fatan za’a samu matsaya.
To sai dai kuma daga bisani shugabar Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare, Uwargida Abike dabiri Erewa ta tabbatar da cewar Hukumomin kasar sun bude kan iyakokin nasu, domin baiwa ‘yan Najeriya damar shiga kasar,bayan da shugaban kasa muhammadu Buhari ya tsoma bakinsa cikin takkadamar.