Hukumar Sadarwa ta kasa, NCC, ta bayyana cewa masana'antun cikin gida sun samu kudaden shiga da ya haura Naira bilyan 55 sakamakon hana shigo da Layukan waya cikin kasar nan.
Idan za a iya tunawa, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a yayin wani bikin baje kolin kayayyakin sadarwa da aka gudanar a shekarar da ta gabata, ya sanar da hana shigo da layukan waya cikin kasar nan.
Da yake tsokaci kan irin nasarorin da hukumar ta samu wajen inganta abubuwan da suka shafi cikin gida, Shugaban hukumar sadarwa ta kasa Farfesa Umar Garba Danbatta, ya ce hana shigo da layukan waya daga kasashen waje, ya temaka wajen saukaka bukatar samun kudin kasashen waje a kasar nan.
Ya kara da cewa haramcin ya temakawa yan kasuwar gida masu kera Layin waya da kansu wajen samun kudin shiga har Naira biliyan 55 .