On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Martanin Atiku Da Obi Kan Rahoton BBC Na Rashin Samun Hujjar Zargin Tinubu Da Mallakar Takardun Karatun Bogi

Tsagin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaran sa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, sun nuna rashin amincewarsu da rahoton BBC na cewa babu wata shaida da ke tabbatar da zargin jabun takardun karatu da ake yiwa shugaba Bola Tinubu.

Tawagar BBC a wani rahoton binciken tantance gaskiyar labari  da aka wallafa ranar Laraba ta ce babu wata shaida da ke nuna cewa Tinubu ya yi karya a takardar shaidar jami'ar Jihar Chicago da ya mika wa INEC.

Da yake mayar da martani, mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa ga Atiku, Phrank Shaibu, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana rahoton na BBC a matsayin wani bangare na shirin farfaganda na gwamnatin Tinubu.

Su kuwa shugabancin jam’iyyar Labour ta bakin mai ba ta shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar, Kehinde Edun, ya ce rahoton da kafar yada labarai ta Burtaniya ta fitar bai girgiza su ba, wanda suka yi nuni da cewa yunkuri ne na kawar da labarin zargin da ake yiwa shugaban kasar.