Manyan hafsoshin sojoji daga wasu kasashen yammacin Afirka sun isa shalkwatar tsaro ta Najeriya da ke Abuja, domin gudanar da wani taro kan mulkin sojoji a Jamhuriyar Nijar.
Manyan hafsoshin sojin da a halin yanzu haka suka iso Najeriya sun hada da Najeriya da Jamhuriyar Benin da Togo da Ghana da Cote’Divoire da Saliyo da Senegal da Liberia da Guinea da Gambia da Cabo Verde.
Taron dai yana gudana karkashin jagorancin shugaban dakarun kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, Janar Christopher Musa.
Idan za’a iya tunawa a ranar Lahadi ne kungiyar ECOWAS ta baiwa ‘yan kasar Nijar wa’adin mako guda su maido da tsarin dimokuradiyya a kasar ko kuma a dauki matakin soji.