Erik Ten Hag ya ce ya gamsu da yadda ya fara takunsa da kafar dama a matsayin mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
Sai dai kuma ya baiyana cewa ba zai bari nasarar da ya samu ta dauke masa hankali ba, bayan doke abokan hamayyar su Liverpool da ci 4 da nema a wasan sada zumunta na share fage da suka yi a Thailand.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara wasan da karfi inda ta samu nasarar jefa kwallaye ukku a ragar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda ya wasa Jadon Sancho da Fred da Anthony Martial suka samu nasarar zura kwallaye a filin wasa na Rajmangala dake Bangkok, duk da kasancewar babu dan wasa Cristiano Ronaldo, wanda yayi balaguro saboda wasu abubuwa da suka danganci iyali.
Dukannin masu horar da kungiyoyin sun sauye-sauye da yawa a cikin mintuna 90, a yayin da mai horaswa Jurgen Klopp na Liverpool ya mamaye wasa a zagaye na biyu kafin dan wasa Facundo Pellistri ya ciwa united kwallo ta hudu.