Dan wasa Rodri ya zura wata kwallo ta ban mamaki sannan Erling Haaland ya sake kafa tarihin zura kwallo a raga yayin da Manchester City ta doke Bayern Munich da ci 3 da nema a ranar Talata a kokarinsu na neman lashe gasar zakarun Turai karon farko.
Haaland, wanda ya ci kwallo ta uku da City ta ci a daren a minti na 76, yana da kwallaye 45 a gasar.
Ayanzu haka dan wasa Erling Haaland yana rike da kambun tarihin dan wasan Premier da ya fi zura kwallaye a gasar.
Shi kuwa dan wasa Romelu Lukaku ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 82, yayin da Inter Milan ta samu damar tsallakewa zuwa matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai bayan ta doke Benfica da ci 2 da nema.