Kungiyar Malaman kwalejin ilimi ta gwamnatin taraiyya dake Bichi a nan Jihar kano,Ta zargi hukumar gudanarwar makarantar da karkatar da wasu kudade wanda Asusun tallafawa manyan makarantu Tetfund ya baiwa makarantar har naira milyan 34 domin biyan hakkokin Alawus na masu sanin makamar aikin koyarwa,domin warware wani batu da ya taso daga hukumar nan ta EFCC.
Kungiyar ta baiyana cewar a baya hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta tilastawa Kwalejin ilimin ta biya dan kwangila wasu kudade amma daga baya ta yanke shawarar karkatar da kudin na Tetfund domin biyan wasu bukatu na daban
Shugaban Kungiyar Malaman kwalejin ilimi ta gwamnatin taraiyya dake Bichi a nan Jihar kano Dr Hussaini Yahya ya baiyana kwalejin a matsayin tamkar wata Sakandire saboda yanayin tabarbarewa data samu kanta a ciki, Inda ya koka kan yadda Daliban makarantar da kuma Malamai basu da wani katin shaida dake tabbatar su dasu a matsayin ‘yan makaranta
Bugu da kari ya ce a Alhamis din makon jiya ne kungiyar ta shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda matsalolin da suka shafi rashin saka kudi a asusun biyan fansho da sauran wasu matsaloli wanda har kawo yanzu babu wani mataki da makarantar ta dauka akan wannan batu.
To sai dai kuma a martanin da shugaban Kwalejin Ilimi ta gwamnatin taraiyya dake garin Bichi a nan jihar Kano, Farfesa Muhammed Fagge ya mayar , Ya baiyana zargin karkatar da kudin da malaman suka yi a matsayin wata jita-jita, Yana mai cewar dole ne a biya malaman da abun ya shafa hakkokinsu.
Kazalika ya zargi kungiyar da rashin bin ka’idar data dace kafin tafiya yajin aikin da suka fara a makon jiya
Dangane da maganata ta ID Card Kuwa, Shugaban makarantar ya baiyana cewar kwalejin tana katin shaida da take dashi, Sai dai akwai bukatar a sake inganta shi , Sai dai kuma ya ce kokarin yin hakan ya gamu da cikas, saboda rashin hadin kai da aka samu.
Farfesa Muhammed Fagge Ya ce rashin saka kudi a cikin asusun biyan fansho ya samo asali ne daga tsarin nan na biyan kudi da gwamnatin taraiyya ke amfani dashi na IPPIS, Kuma kungiyar tana sane da irin kokoarin da aka yi domin magance matsalar.