Kungiyar masu makarantu dake zaman kansu ta kasa ta ce janye tallafin mai da gwamnatin taraiyya ta yi zai sa ta kara yawan kudin makaranta dake take karba daga hannun iyayen yara.
Shugaban kungiyar Chief Yomi Otubela shi ne ya baiyana haka yayin wani taro da aka shirya kai tsaye ta allon gani gaka, kan batun cire tallafin mai , Ya ce duk wani sauyi da za’a samu kan farashin man fetir zai shafi yadda suke gudanar da harkokinsu.
Ya kara da cewar matsalar ba zata tsaya ga iya makarantu masu zaman kansu ba, kasancewar matsala ce da ta shafi al’umma baki daya.
Kazalika kungiyar ta yi kira ga gwamnati data samar da matakan bada tallafin rage radadin janye tallafin ga ‘yan kasa.