On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Majallissar Wakilai Ta Bukaci A Bada Guraben Karatu Ga 'Daliban Najeriya Da Yaki Ya Koro Daga Sudan

Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta umarci dukkanin manyan makarantun kasarnan da su bada guraben karatu ga daliban Najeriya da suka tsere daga yakin Sudan.

Majalisar ta zartar da wannan kudiri ne a zamanta na ranar Talata bayan amincewa da kudirin gaggawa da dan majalisa daga Katsina, Sada Soli ya dauki nauyi.

Soli ya bayar da hujjar cewa yakin Sudan bai kare ba, don haka ba a da tabbacin makomar daliban Najeriya da ke dawowa daga kasar game da karatunsu a matakai daban-daban.

‘Dan majalisar ya ce wasu manyan makarantun sun nuna aniyar daukar daliban amma sai an bukaci gwamnatin tarayya  ta amince mu su.

Bayan wannan kudiri, majalisar ta umarci kwamitinta kan manyan makarantu da ya tabbatar da bin ka'ida tare da bayar da rahoto cikin mako guda don ci gaba da aiwatar da matsayar da aka cimma.