On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Majalissar Wakilan Najeriya Na Cigaba Da Neman A Kamo Gwamnan Bankin CBN

Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai kan sabbin takardun kuɗi na Naira da aka sauyawa fasali ya yi watsi da karin wa’adin kwanaki goma da Babban Bankin kasa CBN ya yi na musayar tsofaffin kudaden Naira.

Tunda farko babban bankin na CBN ya sanya ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira dubu 1. 

Sai dai bayan ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar lahadi a mahaifarsa ta Daura dake Jihar Katsina, gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, yace shugaba Buhari ya bada izinin kara wa'adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu.

A cikin wani martani na  gaggawa, kwamitin wucin gadi wanda shugaban masu rinjayae na majalisar, Hon. Alhassan Ado Doguwa na jam'iyar APC daga Kano ke jagoranta, ya ki amincewa da karin wa’adin, yana mai jaddada cewa dole ne CBN ya yi biyayya ga tanadin sashe na 20 karamin kashi na 3, 4, dana 5 na dokar CBN.

Idan dai za a iya tunawa majalisar, a zamanta na ranar Talata da ta gabata, biyo bayan korafin da ‘yan Najeriya suka yi, ta kafa kwamitin wucin gadi da zai binciki lamarin. 

Doguwa ya ce; “ tsawaita wa’adin kwanaki 10 na canjin  kudin Naira ba shine mafita ba"

Mu a matsayinmu na kwamitin majalisa da kundin tsarin mulki ya tanada, zamu amince da yin bayayya  ga sashe na 20 karamin kashi na 3, 4, da sashi na 5 na dokar CBN. 

Najeriya a matsayinta na mai ci gaban tattalin arziki da dimokuradiyya dole ne ta mutunta tsarin doka, kuma majalisar zata cigaba da yunkurinta na neman kama gwamnan CBN da  gurfanar da shi a gaban kwamitin wucin gadi, acewar Hon Doguwa.

Yace a karkashin shugabancinsa kwamitin zai ci gaba da gudanar da ayyukansa har sai ya biya bukatun ‘yan Najeriya kamar yadda dokokin kasa suka tanada. 

Doguwa wanda ya bayyana karin wa’adin a matsayin siyasa  kawai domin kara yaudarar ‘yan Najeriya da kuma rusa tattalin arzikinsu, Doguwa ya ce dole ne Gwamnan CBN ya bayyana a gabansa ko kuma ya fuskancj kamawa bisa karfin sammacin majalisar da Kakakinta ya sanyawa hannu a ranar Litinin.

Ya kuma ce tsare-tsaren bankin ka  iya kawo cikas ga babban zaben da ke tafe.