Majalisar Malamai ta jihar Kwara ta ja kunnen masu shirin gudanar da bukukuwan addinin gargajiya wanda aka fi sani da Ifa a birnin Ilorin, da su gaggauta janye aniyar ta su batare da bata lokaci ba.
Majalisar ta yi gargadin cewa ba za ta bari a gudanar da bukukuwan ba ta kowacce siga, a fadin masarautun Ilorin da suka hada da Asa sai Moro da Masarautar Ilorin ta gabas sai masarautar Ilorin ta yamma da Ilorin ta Kudu.
Tsohon Grand Khadi na Kotun daukaka karar shari’ar Musulunci ta Jihar Kwara mai suna Mohammed, Shi ne yabaiyana haka a madadin Shugaban Majalisar Malamai kuma Babban Limamin Masallacin Ilorin, Sheik Bashir Salihu a wani taron manema labarai da aka gudanar yau a birnin Ilorin.
Mohammed ya bayyana cewar sama da shekaru 200 aka samu wanzuwar addinin musulunci a birnin Ilorin, A saboda haka gudanar da bukukuwan addinin gargajiyar a ranar 20 ga watan da muke ciki, , yana da matukar hadari ga tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.