A yau ne Majalisar dokokin Najeriya za ta dawo daga hutun kirsimeti da na sabuwar shekara domin cigaba da fuskantar al’amuran da suka shafi kasa baki daya.
Daya daga cikin irin wadannan batutuwa dai shine bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na a sake fasalin hanyoyin lamuni daga babban bankin Najeriya.
A ranar 28 ga Disamba na shekarar 2022, Majalisar Dokoki ta kasa ta zartar da kudurin kasafin kudi na 2023, da kwarya-kwaryan kasafi na 2022 da kuma kudirin kudi na 2022 sannan ta tafi hutu.
A kwanakin baya ne dai Buhari ya bukaci Majalisar Dattawa da ta Wakilai da su amince da sake fasalin tsarin bada rancen kudi da CBN ke amfani da shi wajen bai wa Gwamnatin Tarayya lamuni.