Muddin ba’a samu wani sauyi na gaggawa ba, Majalisar dokoki a Najeriya za ta iya zartar da kasafin kudin 2024 na Naira trilliyan 27.5 a ranar Asabar bayanda ma'aikatu da sassa, da hukumomin tarayya 541 suka kammala kare bangarorinsu.
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Sanata Adeola Solomon, ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa majalisar za ta koma zamanta a ranar Laraba.
A cewarsa, kwamitin nasa ya bude sakatariyar sa, inda dukkanin kananan kwamitocin majalisar dattawa za su mika rahotonsu.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa kwamitin kasafin kudi zai gabatar da rahotonsa a ranar Alhamis, inda ya kara da cewa za a zartar da kasafin a ranar Asabar.