Majalisar dokokin jihar Ondo ta rubutawa babban alkalin jihar, Mai shari’a Olusegun Odusola, da ya kafa kwamitin da zai binciki zargin da ake yi wa mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa na rashin da’a.
A cikin wata wasika mai dauke da sa hannun kakakin majalisar, Mista Olamide Oladiji, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Litinin, majalisar ta ce an ci gaba da yunkurin tsige shi ne bayan karewar umarnin babbar kotun tarayya.
Wannan al’amari dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da majalisar ta sanar da dakatar da shirin tsige shi, biyo bayan kin amincewa da mai shari'a Odusola ya kafa kwamitin a bisa umarnin kotu.