Shirye-shirye da suka kamata sun kammala domin tantance sunayen kwamishinoni da majalisar dokokin jihar Kano za ta yi yau litinin 22 ga watan Augusta kamar yadda aka tsara da karfe goma na safe.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na majalissar Uba Abdullahi ya sanyawa hannu kuma ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ana sa ran kowane mutum da aka aike da sunansa zai je tare da mutane akalla biyar zuwa goma kawai domin tantancewa da nufin kaucewa cunkoso da kuma saukaka wa ‘yan majalisar dokokin tsarin gudanarwa a lokacin.
Idan dai za a iya tunawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika sunayen kwamishinoni ga majalisar domin neman amincewa tare da amincewa da nadin su domin cike gibin da ke akwai a bangaren zartaswar gwamnatin jihar Kano, inda majalisar ta sanya ranar litinin domin gudanar da wannan aiki na tantancewa.
Mutanen da Ganduje ya aike da sunayensu sun hada da:
Hon. Ibrahim Dan'azumi Gwarzo
Hon. Abdulhalim Liman Dan Maliki
Hon. Lamin Sani Zawiyya
Hon. Ya'u Abdullahi Yanshana
Hon. Garba Yusif Abubakar
Dr. Yusif Jibril Rurum
Hon. Adamu Abdu Panda
Hon Saleh Kausani