On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Majalissar Dokokin Jihar Kano Na Duba Yiwuwar Gyara Dokar Ilimi Ta 1963

Majalisar dokokin Jihar Kano ta goma na shirin gyara dokar Ilimi ta jihar wadda aka samar tun shekarar 1963 zuwa matsayin tsarin ilimina duniya.

Shugaban kwamitin kula da harkokin ilimi na majalisar Hon Sulaiman Muktar Ishaq ya sanar da hakan lokacin da yake karbar bakuncin shugaban shirin karfafa ilimin yara mata masu tasowa na AGILE tare da tawagar aiwatar da shirin  a zauren majalisar.

Hon Sulaiman Muktar Ishaq ya ce bisa la’akari da yadda gwamnatin mai ci karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ke tsayin daka wajen bunkasa ilimi, ya zama wajibi kwamitin ya samu kyakkyawar alaka da duk masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da nufin samun ingantaccen ilimi a Jihar Kano.

Ya kuma tabbatarwa shugaban shirin cewa majalisar za ta ba su dukkan goyon bayan da suka dace wajen gudanar da ayyukansu.

Ya kuma yi kira gare su da su tabbatar da gaskiya a duk ayyukansu.

A nasa jawabin shugaban shirin, Alhaji Nasir Abdullahi Kwalli ya ce sun je zauren majalisar ne domin sanar da kwamitin ilimi na majalisar kan tafiyar da shirin AGILE kawo yanzu  wajen tallafawa  rayuwar ‘yan mata ta hanyar ilimi a fadin jihar Kano.

Nasiru Kwalli, wanda ya yi dogon jawabi ya bukaci majalisar ta ba da hadin kai wajen ciyar da jihar gaba, sannan ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa baiwa ilimi fifiko wanda ya bayyana a matsayin hanyar ci gaban al’umma.