Majalisar dokokin jihar Legas ta ce za ta gayyaci kwamishinan ilimi mai zurfi, Mr Tolani Akibu da shugaban jami’ar jihar Legas, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello, da majalisar koli ta Jami'ar da sauran manyan ma’aikata bisa zargin karbar kudi da badakalar takardu da ake yi a makarantar kwanan nan.
Gayyatar dai na da alaka da wani rahoto da wata kafar yada labarai ta intanet ta wallafa a ranar Litinin.
Labarin ya nuna cewa wasu mutane na mallakar takardun shaidar kammala jami’ar jihar Legas wanda duk mai sha’awar zai iya saya a kan Naira milliyan 2 zuwa milliya 3, ya danganta da kwas din da ake so.
A wata sanarwa da mai taimaka wa kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Eromosele Ebhomele ya fitar, shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, ya bayyana cewa tushen labarin na iya zama da shakku kuma ba amintacce ba, yana mai cewa, saboda haka majalissar ta amince ta gayyaci jami’an da abin ya shafa na makarantar domin a iya bankado gaskiyar al'amarin.