On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Majalissar Dattawa Ta Bukaci A Mika Matatun Man Fetur Na Najeriya Ga Hannun Masu Zuba Jari

Majalisar dattawa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mayar da matatun man kasarnan hannun masu zuba jari domin Jinginarwa.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin kudi, Sanata Sani Musa na jam’iyyar APC daga Neja ta Gabas ya yi wannan kira ne a karshen mako a Abuja.

Musa ya amsa tambayoyi daga ‘yan jarida akan hanyar cigaban Najeriya, shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

A cewarsa, matatun man  sun zama nauyi ga gwamnati idan aka yi la’akari da yadda aka gaza gyara su.