Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya bayyana rashin jin dadinsa ganin cewa kawo yanzu jihohi goma sha daya ne suka kada kuri’a tare da yin biyayya ga gyaran kundin tsarin mulkin kasa da majalisar ta yi a farkon wannan shekara.
Sanata Omo-Agege, wanda ya zama shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sake gyaran kundin tsarin mulkin kasa na 1999 bai ji dadin yadda har yanzu jihohi 27 ba su yi nazari da kada kuri’akan kudurorin da aka mika musu watanni shida da suka gabata ba.
Ya bayyana haka ne a ranar Talata a wani taron manema labarai na hadin gwiwa kan gyare-gyaren tsarin mulki da ci gaban da aka samu a majalisar dokokin kasarnan.
‘Dan majalisar mai wakiltar Delta ta tsakiya ya kuma zargi wasu gwamnonin da yin katsalandan a harkokin majalisun dokoki tare da mayar da ‘yan majalisar jiha ‘yan baranda domin cimma burinsu na son rai.