Majalisar zartawa ta kasa ta amince da kasha zunzurutun kudi har sama da naira tiriliyan 2 a matsayin kwarya-kwaryar kasafin kudin shekarar 2023 da muke bankwana da ita.
Da yake jawabi jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwar da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja a jiya, Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki na kasa, Atiku Bagudu, Ya ce za’a yi amfani da kwarya-kwaryar kasafin kudin ne domin gudanar da wasu aiyuka na gaggawa da suka taso.
Ya ce za’a ware wani kaso daga cikin kudin domin cigaba da inganta sha’anin tsaron kasa, wanda ya kai naira bilyan 605 .
Kazalika ya ce za’a yi amfani da naira bilyan 210 domin biyan Karin albashi na wucin gadi na tsawon watanni shida da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatanta alkawari, da kuma gudanar da tsarin nan na baiwa dalibai lamunin karatu.