Majalisar Wakilai ta ce ta kammala shirye-shiryen da suka dace domin raba sabbin motoci ga 'yan majalisar nan da cikin makonni masu zuwa.
Mai magana da Yawun zauren Majalisar, Akin Rotimi, shi ne ya tabbatar da da haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce ‘yan Najeriya sun cancanci sanin halin da ake ciki, kasancewar za'a rika yiwa labarin karin gishiri a shafukan sada zumunta.
Rotimi ya bayyana cewa motocin da za a raba wa ofisoshin Yan majalisar , motoci ne da aka samar dasu domin gudanar da ayyukansu na sa ido, ba wai motocin su bane na kashin kai.
Ya kara da cewa ‘yan majalisar na iya mallakar motocin, ta hanyar biyan kudin motar a Aljihun gwamnati, kafin su zama mallakinsu , idan wa’adinsu ya kare a shekarar 2027, Amma idan ba haka ba sun zama mallakin Majalisar Dokoki ta kasa.