Majalisar wakilai ta fara wani yunkuri na hana ‘yan siyasa da masu ra’ayin siyasar samun mukamai a babban bankin kasa.
Kudirin dokar Babban Bankin kasa ta shekarar 2022 da ake yiwa gyaran fuska wadda ta tsallake karatu na biyu a zauren majalisar a ranar Talata, ta kuma yi tanadin hana masu rike da mukamai a babban bankin kasar shiga cikin harkokin siyasa.
Bugu da kari dokar bankin ta shekarar 2007 tayi tanadin sake saka wasu sharudda da ake bukatar mutum ya cika kafin samun matsayin gwamnan babban bankin ko mataimakinsa ko wani darekta a bankin da sauran wasu mukamai.
Dan Majalisar Sada Soli na jam’iyyar APC daga jihar Katsina wanda ya gabatar da kudirin, ya ce gyaran dokar bankin kasar ba anyi ta bane bisa son zuciya, sai dai kawai domin inganta aiyukan bankin, wanda ya bada misali da yadda gwamnan bankin na yanzu Godwin Emefiele ya garzaya kotu inda yake neman a bashi damar tsayawa takara.