A ranar Talata ne majalisar wakilai ta jingine wani kudiri dake neman Majalisar tayi ikon gaban kanta akan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bayan da yaki amincewa da gyaran fuskar da aka yiwa dokar zabe ta 2022 , domin baiwa masu rike da mukaman siyasa damar zama wakilan jam’iyya.
An janye kudurin ne bayan da mataimakin shugaban majalisar ya ga baiken majalisar wajen daukar matakin, Inda ya baiyana cewa, Dole ne sai an samu kaso biyu bisa ukku na mafi rinjayen yan majalisar da zasu amince kafin zartar da irin wannan kuduri.
Ya shawarci wanda ya gabatar da kudurin Ben Igbakpa, da ya jingine kudurin, kasancewar ya sabawa ka’idojin da ake bi na fin karfin shugaban kasa idan bukatar hakan ta taso
Sama da kwanaki 30 ke nan da tsagin marassa rinjaye a zauren majalisar wakila suka bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rattaba hannu kan wani gyara da aka yiwa dokar zabe ta 2022, amma shugaban kasar bai yi haka ba.