A ranar Litinin ne, Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin ta na cefanar da kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta da kamfanin hakar ma’adinai na kasa domin tuntubar masu ruwa da tsaki.
Majalisar ta amince da kudirin da Abdullahi Ibrahim Halims ya gabatar inda ta gayyaci ministan ma’adinai da karafa domin ya yi mata cikakken bayani kan shirin cefanar da kanfanonin biyu.
Dan majalisar ya baiyana shirin cefanar da kanfanonin da tsakar rana, yayin da ya ragewa gwamnati mai ci kasa da kwanaki 30 wa’adinta ya kare, bai dace ba kuma rashin kishin kasa ne.
Ya yi kira da a samar da wasu tsauraran sharudda koda za’a aiwatar da tsarin ba wai yinshi sake babu kaidi ba.
Daga karshe majalisar wakilan ta umarci kwamitinta mai kula da bangaren ma’adinai da ya yi gaggawar bincike kan lamarin.