Kwamitin kula da Baitul Malin gwamnati na majalisar Wakilai ya fara binciken ma’aikatar aikin Gona ta kasa kan yadda aka bada aikin kwangilar sare wasu dazuzzuka har ta kimanin naira Bilyan 18 da Milyan 900 a lokacin dokar kullen Korona.
Shugaban kwamitin, Oluwole Oke ne ya baiyana haka yayin zaman jin ba’asi da kwamitin ya shirya jiya a Abuja.
Ya kara da cewa abune mai muhimmaci a gano wurare da kuma tasirin da aikin ya haifar, yace a yanzu haka kwamitin ya gaiyaci ma’aikatar da kuma kanfanonin da suka yi kwangilar aikin domin jin nasu ba’asin.
Sai dai kuma kanfanonin da aka turawa katin gaiyatar basu samu damar zuwa wajen ba sannan kuma basu bada wani dalilin yin hakan ba.