On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Hukumar NEPZA Ta Mayar Da Sama Da Naira Biliyan 13 Ga Asusun Gwamnatin Tarayya

Majalisar Wakilai ta bukaci Hukumar kula da futon Kayayyaki ta kasa NEPZA da ta mayar da makudan kudade har Naira biliyan 13 da miliyan 300 da ba a tura zuwa baitul malin gwamnatin tarayya ba.

Kwamitin wucin gadi na majalisar, wanda ya bayar da umarnin a ci gaba da zaman sa a Abuja, ya bukaci NEPZA da ta samar da kwafin takardun hada-hadar kudi da suka hada da kudaden da ta aike wa gwamnati.

Sai dai Daraktan Kudi da Gudanarwa na NEPZA, Oyesola Oyekunle wanda ya bayyana a a gaban kwamitin amadadin hukumar ya ce gwamnatin gwamnatin tarayya bata bin hukumar  bashi yana mai cewa duk kudaden shiga da aka samu ana tura su ga gwamnati.

Sai dai Oyekunle ya shaida wa ‘yan majalisar cewa tun da NEPZA ba ta da cikakken kudin shiga, kashi 25 cikin 100 na kudaden shigar da ake samu ta ke aikawa da gwamnati.