Majalisar dokokin jihar Legas ta amince da naira tiriliyan 1 da bilyan 768 a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2023.
kasafin kudin da aka amince da shi ya nuna cewar za’a kashe Naira bilyan 748 a bangaren aiyukan yau da kullum sai kuma sama da Naira tiriliyan 1 da za’a yi amfani da ita a bangaren gudanar da manyan ayyuka.
A watan Oktoban bana ne, Gwamna Babajide sanwo-olu ya gabatar da kasafin kudin jihar wanda ya kama naira tiriliyan 1 da bilyan 69 ga majalisar dokokin jihar.