Majalisar dokokin jihar Kogi ta gayyaci kamfanin BUA da ke samar da siminti akan wani fili mai fadin kadada dubu 50 da ya mallaka shekaru 10 da suka gabata amma har yanzu ba a biya kudin mallaka ba.
Majalisar ta yi wannan sammacin ne a ranar Litinin a wani taron jin ra’ayin jama’a na daya daga cikin kwamitocin ta na wucin gadi da aka gudanar a wani otal da ke Lokoja sakamakon gobarar da ta tashi a harabar majalisar.
Mataimakin kakakin majalisar, Alfa Momoh-Rabiu, ya karanta sammacin ne biyo bayan jawabin mukaddashin Sabeya janar na jihar Salihu Mustapha.
Shugaban kwamitin wucin gadi na majalissar, Umar Tenimu, yace babban laifi ne ga rukunin kamfaninr BUA ya rike filin sama da shekaru 10 ba tare da biyan kudinsa ba.