Majalisar dokokin jihar Katsina ta bawa kungiyar malaman jami’o’I ta kasa ASUU, reshen jami’ar , Umaru Musa Yar’adua, wa’adin makonni 3 kan su dawo cigaba da aiki a ranar 5 ga watan Satumba.
Shugaban kwamitin ilimi mai zurfi wanda ke wakiltar mazabar Danja, Alhaji Shamsudeen Da'bai, shine ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a birnin jihar.
Ya bayyana cewa, gazawar malaman ta komawa aiki cikin karshen wa’adin mako 3, majalisar zata bawa gwamnatin jihar umarni, kan ta dakatar da albashin su.