Bayan shafe shekara bakwai ana fadi tashin tabbatar da kudirin wata doka, A yanzu haka zauren majalisar dokokin jihar Kano ya amince da kudirin dokar kula da mata masu dauke da juna biyu da kuma kananan yara, a wani mataki na kawo karshe yawan mace-macen mata da ake samu a lokacin haihuwa.
Shugaban kungiyar kare hakkin Dan hakkin da Adam da kuma wayar da kan jama’a,Dr Ibrahim Zikirullahi wanda kungiyarsa ce ta bijiro da kudurin dokar, kuma wani Dan majalisa ya gabatar da kudirin, shi ne ya tabbatar da amincewar kudirin a matsayin doka a ranar Laraba.
Ya fadawa manema Labarai cewar dokar an samar da ita ne domin ta karfafa dokar bangaren zartawa ta kula da mata masu dauke da juna biyu da kananan yara, wadda tsohon gwamnan jihar kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bullo da ita a shekarar 2001.
A cewarsa idan har gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sa hannu kan dokar kafin saukarsa daga kan mulki, Zata temaka wajen inganta kula da lafiyar masu karamin karfi a jihar kano.
Daga nan sai ya yabawa zauren majalisar dokokin jihar da sauran abokan hulda wadanda suka aiki ka fada da ka fada domin samun tabbatuwar dokar, Yana mai cewar tarihi ba zai manta da gwamna Ganduje ba idan har ya sa hannu kan dokar kafin ranar 29 ga watan da muke ciki.